Wasu ‘yan bindigaAn sun kai hari ofishin‘ yan sanda da ke karamar hukumar Ohaukwu a jihar Ebonyi, inda suka sallami duk wadanda aka tsare a ofishin.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, harin ya faru ne da sanyin safiya yau Litinin.
Loveth Odah, jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Ebonyi, ta tabbatar da afkuwar lamarin, amma bai yi cikakken bayani ba.
Jaridar Daily Trust ta bayya ne cewa, ‘yan bindigar sun kona motocin sintiri na rundunar yan sandan yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun yi Garkuwa da Hamshakin Dan Kasuwa a Jihar Taraba
Jami’an tsaro na sha fama da boren da kuma tashin hankali da ake zargin tsagerun ‘yan kungiyar aware na IPOB ke kaddamarwa a yankin Kudu Maso Gabashin Nigeria.