Gwamnatin Jihar Sakkwato ta amince ta ware sama da naira biliyan daya domin gina wata cibiyar wasanni da kuma wani rufaffen ɗakin wasa a babban birnin jihar.
Muhammad Bello, mai bai wa Gwamna Aminu Tambuwal shawara kan harkokin yaɗa labarai shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda sanarwar ta ce gwamnatin ta amince da hakan ne a ranar Laraba.
Bello ya ƙara da cewa za a kashe biliyan 1.2 na kuɗin da Majalisar zartarwar jihar ta sahhale wurin gina filin wasan, inda za a kashe miliyan 447 a ginin rufaffen ɗakin wasan.