Shahararren Malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta hanzarta sakin tsohon mai bai wa tsohon Shugaba kasa Goodluck Jonathan shawara a kan harkokin tsaro, Kanar Sambo Dasuki, daga gidan yari, ba tare da wani bata lokaci ba. Haka nan malamin ya yi kira ga gwamnatin ta tarayya da ta hanzarta sakin jagoran ’yan uwa Musulmi na Nijeriya da a ka fi sani da Shi’a, Sheikh Ibraheem Zakzaky. Sheikh Gumi ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ke rufe karatun tafsirinsa na wannan shekarar a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna ranar Asabar, inda ya ce, lallai akwai bukatar gwamnati ta bi umarnin kotu. Gumi ya ce, sam babu wata hujja ta cigaba da tsare mutanen biyu bayan kotu ta bayar da umarnin bayar da belinsu. Ya ce, kamata ya yi gwamnatin tarayyar ta sasanta ne da Sheikh Zakzaky a maimakon cigaba da tsare shi, kuma akwai bukatar gwamnati da ta duba maganar Kanar Sambo Dasuki ta kuma sake shi ba tare da bata lokaci ba. “Kamata ya yi su sake shi, sai gwamnatin ta sasanta da shi, ya kuma kamata gwamnati ta fahimci cewa, sam bai kamata ta na kin yin biyayya ga umurnin kotu ba,” in ji malamin ya na mai karawa da cewa, “idan har gwamnati da kanta za ta rika kin yin biyayya ga umurnin kotu, hakan ya na nufin haramtattun kungiyoyi ma su na da damar kin yin hakan. “Amma babu ta yadda za a halasta ta’addanci. Don haka, tilas ne gwamnati ta bayar da misali ta hanyar sakin su, musamman shi Kanar Sambo Dasuki.” Malamain addinin Musuluncin kuma ya yi kira ga kasashe irin su kasar Saudiyya, Turkiyya, Misra da su guji kamawa da kuma tsare malaman addinin Musulunci, saboda bambancin fahimtarsu kurum.