Kocin kungiyar kwallon kafa ta Rangers International dake garin Enugu Salisu Yusuf ya datse kwantiragin sa na kakar wasa biyu daya kulla da kungiyar, yayin da yanzu zai koma Horas da kungiyar Kano pillars.
Salisu ya jagoranci kungiyar da akewa lakabi da “The Flying Antelopes”a kakar wasan data gabata, yayin da Rangers din ta karkare a mataki na 7 da maki 62 bayan buga wasa 38, a gadar Premier gida Nigeria.
Yusuf Salisu Ya horas da kungiyoyin irinsu Enyimba, da Lobi Stars da kuma FC Taraba.
Sai dai babban aikin da ke gaban salisu a aikin na Kano pillars shine, lashe kofi da kuma samun tikitin halartar gasan wasannin Afirika.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun sace Sarkin Bungudu
Yusuf wanda ya taba zama mataimakin kociyan Tawagar Super Eagles, yanzu kuma coach Ibrahim dake rike da kungiyar shi ne zaiyi mishi mataimaki.
A wani labarin na daban
Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani limamin cocin Anglican, Emeka Merenu, wanda ya fito daga kauyen Amorji Agbomiri dake karamar hukumar Nkwerre ta jihar Imo.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutane da ake zargin membobin kungiyar Tsaro ta Gabas ESN ne, ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra IPOB suka kashe shi.
Sai dai wani dan majalisar da ke wakiltar karamar hukumar Nkwerre a jihar Imo, Obinna Okwara, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
A cewarsa, an kashe limamin cocin Emeka Merenu bayan kisan gilla da yayi a garin Orsu Iheteukwa,dake cikin karamar hukumar Orsu ta jihar Imo da sanyin safiyar ranar Talata.
Ya kara da cewa an kashe limamin ne bisa zargin da ba shi da tushe wanda a yanzu haka sojoji sun killace wajen dan tabbatar da kare cocinsa da makarantar sakandare dake karkashin kulawarsa.