• About Us
  • Blog
  • Gwamnatin Jihar Kano ta ce ana gabda fara ginin masana’antun Iskar Gas a Jihar
  • Home
Monday, March 20, 2023
  • Login
Dimokuradiyya
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
Dimokuradiyya
No Result
View All Result
Home Uncategorized

Sallar Idi: An Horar Da ’Yan Agaji 300 Don Samun Tsaro A Jihar Bauchi

Mustapha Haruna Dabai by Mustapha Haruna Dabai
May 20, 2019
in Uncategorized
Reading Time: 4 mins read
1 0
0
2
SHARES
18
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

A jiya Lahadi ne aka kawo karshen taron bita don sanin makamar aiki ga ‘yan Agaji da ‘yan Banga su dari uku (300) da wani bawan Allah ya dauki nauyin horar da su domin sanin dabarbarun yadda za su shawo kan cinkoso, kare lafiya da dukiyar jama’a gabanin da kuma bayan lokacin bukukuwan karamar sallah a jihar Bauchi. Horaswa kan sanin dabarbarun gudanar da aiki domin inganta zirga-zirga a hidimar sallar wanda wani mai tallafi kuma asalin dan jihar Bauchi, Janaral Manaja a hukumar Albarkatun Mai ta Kasa wato (NNPC)  Alhaji Bala Wunti ya dauki nauyin gudanarwa, inda aka zakolo masu amsar horon su 300 daga kungiyoyin agaji na musulmi daban-daban da suka zarce kungiyoyi 10 a fadin jihar ta Bauchi. Ababen da suka samu horon sun hada da warware cinkosan ababen hawa, bayar da agajin gaggawa idan bukatar hakan ta taso, kare lafiya da zirga-zirgan massalata a lokacin bukukuwan sallah. Da ya ke nasa jawabi a wajen taron amsar horaswar, Hakimin cikin garin Bauchi Alhaji Nura Adamu Jimba ya bayyana cewar wannan horaswar zai taimaka gaya domin kuwa ‘yan agajin suna bukatar karin sani kan hidimar inganta aikinsu domin samun dabararrun aiki. Nura Jumba ya shaida cewar a lokacin bukukuwan sallah ana samun cinkoso ababen hawa da kuma na mutane musamman a ta titin Bakaro da na Kofar Gombe ga wadanda suke son zuwa sallah, don haka ne ya bayyana cewar samun horon tamkar taimakon dukkanin masallata ne. Da ya ke bayani kan aikin ‘yan Agaji, Jumba ya shaida cewar aiyukan ‘yan agaji aiki ne mai matukar muhimmanci a cikin al’umma, inda ya nunar da cewar suna gudanar da aiyukansu ne kyauta domin neman lada a wajen Allah, yana mai misaltasu da jami’an tsaro na gwamnati kamar ‘yan sanda da cewar koda aikin addini za a yi sai an basu dan tallafi kafin su zo su gudanar da aiyukansu illa aikin ranar sallah kadai da suke yi kyau, “Amma ku ‘yan agaji dukkanin aiyukan da kuke gudanarwa ga jama’a kyauta ne, wannan taimakon ladarsa a wajen Allah kuke riska, ina jawo hankalinku ku ci gaba da rike aikinku bil-hakki domin yi wa jama’a hidima a kowani lokaci,” A cewar shi. Ya yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga dukkanin ‘yan agaji da su bayar da hadin kai wa jami’an tsaro irin su ‘yan sanda da hukumar kiyaye hadura domin hada hanu waje guda don inganta aiki, yana mai shaida cewar samun kungiyoyin agaji zai taimaka gaya wajen kyautata tsaro da lafiyan jama’a. Shugaban Gammayar kungiyoyin ‘yan agaji na jihar Bauchi Alhaji Bala Ibrahim Libidin Bauchi ya gode wa bawan Allah da ya dauki nauyin shirya wannan bitar wacce a cewarsa zai kawo ci gaba wa al’umman musulmai wajen samar da hanyoyin yi musu hidima sosai. A cikin makalar da ya gabatar kan aikin jinkan al’uma, Libidin Bauchi ya kuma bukaci wadanda abun ya shafa musu hanu da shuni da kuma gwamnati da su yi koyi da hakan, “Bara da bariya an yi irin wannan horon daf salla, a bana kuma sai aka inganta horarsar domin muhimmancinsa. Muna godiya kwarai da gaske Allah ya saka wa wannan bawan Allah ya kuma taimakesa, muna fatan a badi ya fadada shirin ya fi haka,” In ji Libidi. Da ya ke jawabi a wajen, Janaral Manaja na NNPC Alhaji Bala Wunti ya shaida cewar manufar shirya taron shine domin a samar wa ‘yan agajin ilimin sanin makamar aiki kamar yadda ya dace, yana mai shaida cewar mafiya yawan kungiyoyin agaji na addini basu da cikakken ilimin yadda za su bayar da agajin gaggawa ko kuma magance wani matsalar masu kawo cikas a lokacin da suke bakin aikinsu, sai ya bayyana cewar hakan ne ya sanya shirya taron domin a samar da ci gaba. GM din wanda ya samu wakilici daga Isyaka Isma’il Wunti (Wani kwararren dan jarida a Bauchi) ya yi fatan dukkanin wadanda suka samu horon za su yi aiki da ababen da suka koya domin cimma burin da aka sanya a gaba. Wunti ya shaida cewar Bala Wunti ya shafe shekaru uku kenan yana gudanar da irin wannan aiki, ya kuma bayyana cewar, “Wannan shine karo na uku da ake shirya irin wannan bitar, Babbar manufar shiryawar shine domin a samu hadin kai a tsakanin ‘yan agajin nan wajen gudanar da harkokin sallah gabanin da bayan sallah lafiya. “Wannan horo zai taimaka musu gaya ta hanya za su samu ilimin aikin da suke bayarwa na tsaro, don shi hidimar tsaro na da dan sarkakiya wani lokacin a maimakon mutum ya gudanar da aikin taimako sai ya je ya fada aikin da bai shafeshi ba. “Don haka wannan horon ya ilmantar da su iyaka matsalarsu a matsayinsu na ‘yan agaji wanda hakan zai kawo gyara wajen fadawarsu cikin aiyukan da bai shafesu ba,” Inji Bala Wunty ta bakin Isyaka Isma’ilin Wunty Wakilinsa. Daga karshe dai Bala Wunti ya shaida cewar babbar fatarsa shine dukkanin wadanda suka samu horon su koyar da wasu kana su yi aiki da hakan domin cimma nasarar da aka sanya a gaba, “Kwararru daga fannini daban-daban ne suka gabatar da makala a wajen wannan taron bitar, don haka fatanmu a nan shine wadanda suka samu horon su yi aiki da ilimin da suka samu,” Inji Isyaka. Wakilinmu ya shaida mana cewar bayan kammala taron bita don sanin dabarbarun aiki wa ‘yan agaji su dari 300, Bala Wunty ya raba wa kowani daya daga cikinsu buhun shinkafa guda daya, da kudi naira dbu biyar-biyar 5,000 lakadan ga kowannensu, “Sannan ga mata wadanda suka samu horon mun kara musu da Zanin Atafma mai tsada da za su kara a kan shinkafa da kudin da aka rabar musu domin su samu zarafin dinkawa a sallah da kuma shagulgulan sallah lafiya,” Inji Isma’iln Wunty. Wasu daga cikin wadanda suka samu horon sun shaida godiyarsu hade da shan alwashin koyar da masu mukami na kasa da su ilimin da suka samu domin fadada ilimin zuwa ga saura; “Ban taba ganin mutumin da ya tara ‘yan agaji mutum dari har uku ya dauki nauyin komai da komai domin kara musu ilimi kan aikinsu, kuma bai barsu haka nan ba, sai da ya dauki naira dubu biyar-biyar ga kuma buhun cinkafa ga kowani wanda ya zo ya halarci wannan taron bitar wannan muna godiya kwarai a bisa wannan,” In ji wani dan Agajin kungiyar Izala Musa Jabir. Ita ma wata ‘yar Agaji ta shaida wa ‘yan jarida farin cikinta bayan da ta amshi kyautar kayyakin da aka mika musu bayan samun horon, “Sunana Maryam Al-Amin, godiyarmu za mu ne don kawai nuna farin cikinmu, amma sakayyar wannan aikin sai a wajen Allah. Ko ba komai haduwar ‘yan agaji daban-daban a nan an samu hadin kai, kuma ga ilimin da muka samu sanan aka bimu da kyauta, lallai mun ji dadi sosai Allah saka masa,” In ji Maryam.

Previous Post

Tsakanin Tsige Sarki Sanusi Da Tsinka Masaurautar Kano Wanne Ya Fi Rangwame?

Next Post

An Bukaci EFCC Da Ta Binciki Yadda Aka Raba Tallafin IIRO Ga Marayu A Bauchi

Next Post

An Bukaci EFCC Da Ta Binciki Yadda Aka Raba Tallafin IIRO Ga Marayu A Bauchi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result
Arabic Arabic English English French French Hausa Hausa
  • Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    2455 shares
    Share 982 Tweet 614
  • Da Ɗumi-Ɗuminsa: Ƙazamin Rikici Ya Kaure Tsakanin Shugaban Ƙungiyar CAN Da Isa Ashiru Kudan

    1995 shares
    Share 798 Tweet 499
  • Sai na yi lalata da kai na kwanaki 4 babu ƙaƙƙautawa sannan zan taimaka maka, Wata mata ga saurayi

    1693 shares
    Share 677 Tweet 423
  • Ga Irinta Nan: Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Ƙi Amsar Cikin Da Ya Ɗirka Mata

    1365 shares
    Share 546 Tweet 341
  • CBN Ya Sake Fitar Da Sabbin Bayani Kan Dawo Da Tsofaffin Takardun Kudin Naira

    1592 shares
    Share 637 Tweet 398
INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato

INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato

March 20, 2023
PDP Ta Lashe Kujeru 28 Na Majalisar Dokoki, Yayin Da APC Ta Tsira Da Hudu

PDP Ta Lashe Kujeru 28 Na Majalisar Dokoki, Yayin Da APC Ta Tsira Da Hudu

March 20, 2023
Bayan Faduwa A Zaben Sake Darewa Kujerar Sanata Nnamani Ya Bar PDP

Bayan Faduwa A Zaben Sake Darewa Kujerar Sanata Nnamani Ya Bar PDP

March 20, 2023
Mohammed Ya Sake Lashe Zaben Gwamna Karo Na Biyu A jihar Bauchi

Mohammed Ya Sake Lashe Zaben Gwamna Karo Na Biyu A jihar Bauchi

March 20, 2023
Da Dumi-Dumi: Ɗan Takarar APC Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Sakkwato

Da Dumi-Dumi: Ɗan Takarar APC Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Sakkwato

March 20, 2023
An Kaiwa Jami’an EFCC Hari a Kaduna

Da Ɗumi-Dumi: INEC Ta Ayyana Zaben Gwamna Kebbi da ‘Inconvlusive’

March 20, 2023
INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato
Labarai

INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato

March 20, 2023
PDP Ta Lashe Kujeru 28 Na Majalisar Dokoki, Yayin Da APC Ta Tsira Da Hudu
Labarai

PDP Ta Lashe Kujeru 28 Na Majalisar Dokoki, Yayin Da APC Ta Tsira Da Hudu

March 20, 2023
Bayan Faduwa A Zaben Sake Darewa Kujerar Sanata Nnamani Ya Bar PDP
Labarai

Bayan Faduwa A Zaben Sake Darewa Kujerar Sanata Nnamani Ya Bar PDP

March 20, 2023
INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato

INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato

March 20, 2023
PDP Ta Lashe Kujeru 28 Na Majalisar Dokoki, Yayin Da APC Ta Tsira Da Hudu

PDP Ta Lashe Kujeru 28 Na Majalisar Dokoki, Yayin Da APC Ta Tsira Da Hudu

March 20, 2023
Bayan Faduwa A Zaben Sake Darewa Kujerar Sanata Nnamani Ya Bar PDP

Bayan Faduwa A Zaben Sake Darewa Kujerar Sanata Nnamani Ya Bar PDP

March 20, 2023

Twitter

Archives

Recent Posts

  • INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato
  • PDP Ta Lashe Kujeru 28 Na Majalisar Dokoki, Yayin Da APC Ta Tsira Da Hudu
  • Bayan Faduwa A Zaben Sake Darewa Kujerar Sanata Nnamani Ya Bar PDP

Quick Links

  • Tsaro
  • Siyasa
  • Labarai
  • Wasanni
  • Kasuwanci
  • Rikicin Duniya

Contact Us

info@dimokuradiyya.com.ng

0809 912 4425 +234 809 912 4425

No. 218 Mogadishu layout Kaduna City Center Ahmadu Bello way kaduna. Kaduna, Nigeria 800273

Copyright © 2022 Dimokuradiyya Media Services LTD.

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio

Copyright © 2022 Dimokuradiyya Media Services LTD.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In