Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo, a ranar Laraba, ya bayyana cewa gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele, bai cancanci shugabancin babban bankin ba.
A cewar Akeredolu, ya kamata a kori gwamnan CBN daga ofis lokacin da ya nuna sha’awar tsayawa takarar tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.
KU KARANTA: Matakin CBN Na Kin Karɓar Tsohon Kudi Tamkar Cin Fuska Ne Ga Kotun Koli – Lauyoyi
Gwamnan ya kara da cewa da rashin nasarar da Emefiele ya yi na tsayawa takarar fidda gwani zai tabbatar da cewa ya kawo cikas a zaben 2023.
Akeredolu ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar mambobin kungiyar matasa na kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa, PCC, na jam’iyyar APC karkashin jagorancin Seyi Tinubu.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa kimar APC ta ragu matuka sakamakon matsalolin naira da karancin man fetur a kasar.
Ya kuma bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya umurci Emefiele da ya sauya manufar sake fasalin naira a yanzu, ya kara da cewa ya kamata a bar sabbin da tsofaffin takardun kudi su kasance tare.
Akeredolu ya lura cewa duk da umarnin kotu da ke akwai, tsoffin kudin da alama sun daina zama doka a cikin ƙasar.
A nasa bangaren, Seyi Tinubu, jagoran ganin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, yayi nasara, ya yabawa Akeredolu bisa jajircewarsa wajen ci gaban matasa a jihar.
A wani labarin kuma: Yanzu-Yanzu: Buhari Na Jagorantar Taron Majalisar Ministocin sa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya fara jagorantar taron majalisar zartarwa ta tarayya a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa, Abuja.
Sai dai kuma Buhari ya isa zauren majalisar ne da misalin karfe 11:00 na safe, kimanin sa’a daya bayan karfe 10:00 na safe.