Sama da Ƴan Najeriya 3,600 zasu rasa halartar Hajjin Bana
Kimanin Musulmi miliyan ɗaya a yau zasu halarci wajen gudanar da tsayuwar Arfa, ibada mai matuƙar mahimmanci ga masu aikin Hajji wanda ke gudana a Saudiyya.
Amma kimanin ƴan Najeriya 3,660 wanda suka tsara zuwa tafiyar ba zasu samu dama ba, bayan jirgi na ƙarshe ya tashi a ranar Alhamis, ya bar su, suna jimami.
KARANTA WANNAN LABARIN: Haɗin Kai Tsakanin Hukumomi Yana Da Muhimmanci Wajen Haɓaka Haraji –Shugaban FIRS
Wannan shine hajji na farko tun bayan da Cutar Covid-19 da ta kawo tsaiko a shekarar 2020, haka a Shekarar 2020 da 2021, mazauna Saudiyya kaɗai suka gudanar da Hajjin.
Wannan shekarar, kimanin ƴan Ƙasar waje 850,000 da ƴan gida 150,000 aka tsara zasu gudanar da Hajjin. Wannan abun a koka ne, bayan kusan Miliyan 2.5 da suka gudanar da Hajji a Shekarar 2019.
Nijeriya ta samu ƙarin lokaci, bayan ta kasa kammala kwashe Mahajjatan ta. Ƙasar dai an bata Kujeru dubu 43,008 domin Mahajjata.
Amma daga lokacin da Saudiyya ta kulle shigar da Mahajjata, Daily Trust ta gano cewa kimanin Maniyyata Aikin Hajji 2,550 da suka biya ta hanyar Hukumomin kula da Aikin Hajji na Jihohin su ba zasu samu damar halartar Hajjin ba. Wannan ƙari ne bisa ga wanda suka kasa samun visa ta zuwa kasar.
Wani a Hukumar tace Hukumar ta bada visa ga Mahajjata 33,936 Wanda suka biya ta hanyar Hukumomi na Jihohi daga ciki an kwashi 31,386.