Kwamitin da Gwamnatin Jihar Zamfara ta kafa wanda tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Wakkala yake jagorancin domin zakulo sama da fadi da rub da ciki da dukiyar gwamnatin jihar.
Kwamitin ya fara aiki inda ya zakulu wata badakalar kudi kimanin N100bn naira bilyan dari tayi batan dabo a aljihun tsohon gwamnan jihar Yari.
Wadannan makudan kudade an fitar da su ne da zimmar cewa an Gina borehole wato tuka tuka a fadin jihar Zamfara wanda kowane daya ya kai kimanin N325m miliyan dari da ashirin da biyar.
Kwamitin ya tabbatar da cewar har yanzu Ana cigaba da binciken yadda waccan gwamnatin ta gudanar da mulkin jahar da kuma yanda wasu bilyoyin kudi su ka bata da zimmar cewa an gudanar da wasu ayyuka a jahar.
Sai dai abin da ya bayyana akan wannan badakala shine da akwai lauje cikin nadi, babu aiki babu daliiin shi, kuma babu kudin shiru wai Malam ya ci shirwa, bincike zai tabbatar da yanda abun ya wakana.