Ƙungiyar Kare Haƙƙin Bil’adama ta Duniya mai suna Save the Children International, tace auren wuri na kashe mata sama da 60 a duk rana.
Ƙungiyar ta naƙalto wani rahoto da yayi ƙiyasin cewa kashi 44 na ƴan matan Nigeria nayin Aure ne kafin cikar su shekaru 18, wanda wannan shine auren wuri da akafi yi a duniya baki ɗaya.
Ƙungiyar ta bayyana haka a cikin wani jawabi data fitar a ranar Litinin da daddare, wanda Shugaban ta ya sanya wa hannu Inger Ashing, domin bikin murnar ranar ƴaƴa mata ta duniya ta shekarar 2021.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rashin Ƙwazo: Ganduje ya kori Mu’azu Magaji Ɗan sarauniya daga muƙamin sa
Sanarwar ta ce “yawan matan da ake aurar wa da wuri, akwai yiwuwar ya ragu, domin matan Nigeria na zama a wani yanayi na matsatsi.
“A dalilin faɗan ƴan bindiga dadi, da faɗace-faɗacen al’umma, da garkuwa da mutane, da gudun hijira, da cutar Covid-19, da matsin tattalin arziki, rayuwar miliyoyin mata yana jefa su cikin wani hali, ciki harda rashin samun wadataccen ilmi, da abinci, da rashin kare masu haƙƙin su, da sauran su, inji rahoton akan yara mata na Nigeria.
“Kimanin yara mata dubu 22,000 ke mutuwa kullum a dalilin ciki, da haihuwa wanda duk sanadin su auren wuri ne, inji wani sabon bincike da ƙungiyar kiyaye haƙƙin mata ta saki.
“Ninkuwar adadin yara matan da ake yiwa auren wuri a duniya, yankin Afirka ta Yamma data tsakiya, na samun kimanin mata dubu 9,600 dake mutuwa sakamakon auren wuri a duniya,