Cocin Eklesiyya ‘Yan’uwa ta Nigeria (EYN), ta bayyana cewa sun rasa mutum 8,370 sakamakon hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram.
Cocin EYN ya kwashe fiye da shekara 97 da kafa shi a garin Garkida, inda a halin yanzu yake da hedikwata a gari Kwarhi dake jihar Adamawa.
Cocin sun tabbatar da hakan ne a wani taron ‘yan jarida da suka kira a garin Yola a jiya kamar yadda jaridar Daily Trust suka labarto, inda suka tabbatar da cewa daga cikinsu akwai Fastoci Takwas da Boko Haram ta kashe.
Rabaran Joel Billi, shugaban Cocin EYN, shi ne ya karanta takardar bayaninsu ga taron ‘yan jaridar a babban Cocinsu dake Jimeta a Yola, inda ya ce EYN shi kadai Cocin Kiristoci da barnar Boko Haram ya fi shafa. “Inda fiye da membobinmu 700, 000 suka yi gudun hijira, inda Cocinmu bakwai cikin 60 harin Boko Haram din ya shafe su a yankuna daban-daban.” inji shugaban EYN din.
Ya tabbatar da cewa ‘yan matan makarantar Chibok 217 cikin 276 da Boko Haram suka sace, membobin cocin EYN ne. Inda ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Adamawa, Borno da Yobe da su kwato sauran ‘yan matan dake hannun Boko Haram din ciki harda da Leah Sharibu, Alice Loksha da sauran su.