By Ishaq Dabai
Akalla mutane 55 ne suka mutu sakamakon hadarin jirgin ruwa a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, kamar yadda hukumomin yankin suka tabbatar dpa ranar Juma’a.
Mutane da yawa har yanzu sun bace, in ji kakakin hukumar bada agajin gaggawa Jose Misiso.
Jirgin ruwan wanda yake cike da mutane yana tafiya ne a kan Kogin Kwango kuma ya kife kusa da garin Bumba da ke arewacin lardin Mongala da sanyin safiyar ranar Laraba.A cewar kakakin, kawo yanzu mutane 30 ne aka ceto daga cikin ruwan.
Ba a san takamaiman adadin mutanen da suka bace ba, yayin da hukumomi suka ce har yanzu ba a ga fasinjoji 75 ba, wadanda suka tsira sun yi magana kan cewa jimillar mutane 400 ke cikin jirgin.
Kogin Kwango da hanyoyin dake ƙarƙashinsa wata muhimmiyar hanyar zirga zirga ce ga mutane da yawa a Kongo saboda rashin ingantattun hanyoyin mota a cikin ƙasar, galibi jiragen ruwa suna diban mutane fiye da kima duk da haka, kuma hadurra na faruwa.