Sama da Mutane goma suka rasa rayukansu sanadiyyar hatsari, Kasuwar Bode
A kalla mutane goma suka mutu a yau Lahadi a kasuwar Bode a Ibadan inda wata babbar mota cike da lodin Raguna ta kucce.
Mai magana da yawun Yan sandar Jahar Adewale Osifeso, shine ya tabbatar wa Jaridar Dailytrust aukuwar lamarin inda yace mutane biyar suka mutu.
Osifeso yace da kuma mutane da dama wadanda suka sami raunuka, yace zai tuntubi mai rahotanmu bayan ya kammala tattara bayanai.
Kamar yadda mai rahotanmu yace wata babbar mota dauke da lodin gas tafito daga Idi-Arere kanta ya kwace tai cikin kasuwa.
Jami’an kwashe gobara nanda nan suka zo don dakatar da yawan barna da hatsarin ka iya haddasawa.