Hukumar yaki da cututtuka masu yaɗuwa a Nijeriya, NCDC, ta ce mutum 103 ne suka mutu sakamakon cutar korona.
A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter a daren Alhamis, NCDC ta ƙara da cewa cutar ta korona ta kama 3145 baki daya ya zuwa daren. A cewarta, mutum 534 ne suka warke daga cutar kawo yanzu.
Cikin mutanen da suka mutu, mutum 31 daga Legas suke, mutum 13 daga Kano, Abuja tana da mutum 4.