By Ishaq Dabai
A ƙalla mutane 10,000 ƴan asalin Jihar Katsina ne ke aikin haƙar Zinare a Ƙauyen Kwandago dake Jamhuriyar Nijar.
Shi dai wannan yanki na Kwandago dake da albarkacin ma’adanin zinare, yana a ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Dan Issa, ta Jihar Maradi dake Jamhuriyar Nijar.
Yankin na Kwandago yana da iyaka da Karamar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina, kuma yanada nisan kilomita kusan 20 daga garin Kukar Babangida dake Kan hanyar Katsina zuwa Jibia.
Wakilin Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa The Fact 24 daya ziyarci wannan yanki da ake aikin haƙar zinarin, ya bayyana cewar bayan ƴan asalin Jihar Katsina, akwai sauran mutane dake aikin haƙar zinarin daga wasu Jahohin Najeriya.
Kamar yadda alkalumma suka nuna, kashi 75 zuwa 80 na mutanen daKe aikin haƙar zinarin da masu kasuwanci a yankin, ƴan asalin Najeriya ne wanda yawansu ba zai gaza su dubu 20,000 ba.
Kazalika, an samu jama’a sun tsunduma a aikin haƙar zinarin, inda wasu kuma na aikin fasa dutse, a yayinda wasu kuma ke aikin ɗura ƙasa a buhunna, wasu kuma na aikin wankar dutse da ƙasa da aka saro daga ramukan haƙar zinarin.
Har ila yau, wasu mutanen sun tsunduma a aikin debo ruwa a jarkoki wanda akan sayar da shi akan kudi naira 300 kowace jarka, baya ga masu ɗaukar duwatsu da ƙasa zuwa wurin wanki dake garin Ɗan Issa.
A halinda ake ciki dai al’umma nata yin tururuwa zuwa wannan yanki domin neman abin sakawa bakunan salatinsu.