By Abbas Yakubu Yaura
Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa sama da yara 45,000 ne aka sako daga gidajen gyaran hali wadanda ake tsare dasu yayin barkewar annobar cutar COVID-19.
Kungiyar tabayyana hakan ne a ranar Lahadin data gabata a cikin rahotonta mai taken, ‘Fiye da yara 45,000 da aka sako daga tsare a lokacin barkewar cutar ta COVID-19 wanda hakan wata shaida ce dake nuna cewa akwai yuwuwar samun mafita na samun adalci ga yaran inji – UNICEF.
A cewar rahoton, wanda aka fitar gabanin taron Majalisar Dinkin Duniya kan yiwa ya Adalci, sama da yara 261,000 ake tsare da su a fadin duniya.
UNICEF ta kuma lura da cewa bayan data ja hankali kan karuwar hadarin kamuwa da cutar COVID-19 sakamakon cunkoso a gidajen yari, a kalla kasashe 84 sun amince da sakin dubban yaran da ake tsare dasu tun watan Afrilun shekarar 2020.
“Mun dade da sanin cewa tsarin shari’a basu da kayan aiki don kula da takamaiman bukatun yara – lamarin dake kara ta’azzara cutar ta COVID-19,” in ji Babban Daraktan UNICEF, Henrietta Fore.
Ta ci gaba da cewa, “Muna yabawa kasashen da suka yi biyayya ga kiran da muka yi, suka sako yara da suke tsare.”Ta hanyar kare yara daga yanayin da zai iya jefa su cikin mummunar rashin lafiya, waɗannan ƙasashe sun sami damar shawo kan juriya na jama’a da kuma haifar da sababbin hanyoyin magance adalci da suka dace da shekaru.
A matsayinmu na masu tsara manufofi, masu shari’a, malamai, kungiyoyin farar hula, da yara da matasa dake taro a Majalisar Dinkin Duniya a wannan makon, dole ne mu yi aiki tare don kawo karshen tsare yaran,” in ji Fore.