Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta samar da ma’aikatar da za ta riƙa kula da dabbobi a faɗin ƙasar nan wanda hakan zai basu damar bai wa ƙasar nan gudunmawa wajen farfaɗo da tattalin arziƙi.
Sakataren ƙungiyar Alhaji Usman Ngelzarma ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Alhamis da ta gabata.
https://dimokuradiyya.com.ng/2023-tinubu-da-inyamurai-ba-zasu-taɓa-mulkar-najeriya-ba-miyetti-allah/
Ya ce, a ƙasashen yammacin Afrika sun samar da irin waɗannan ma’aikatu wanda hakan ya taimaka musu wajen magance matsalolin da suke fuskanta.
Alhaji Usman ya ƙara da cewa, ɓangaren da ke kula da su ƙarƙashin ma’aikatar aikin noma ba zai iya basu damar shiga wajen magance matsalar da ƙasar nan ke fuskanta ba, saboda haka yanzu lokaci yayi da Najeriya za ta amfana daga ɓangaren kiwo.
Cikin matsalolin da ya lissafo ya ce suna fuskantar satar dabbobi da yin garkuwa da mutane da rikicin makiyaya wanda ya sanya har yanzu basa samun damar kula da rumbunan adana kayayyakin su.