Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima, a matsayin daya daga cikin nasarorin da Najeriya ta samu “tun farkon dawowar dimokuradiyya.”
Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin sakon taya murna da Kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar a Abuja domin bikin tunawa da ranar Haihuwar Shettima na cika shekaru 55 a ranar Alhamis.
Shugaba Buhari ya ce: “Ina alfahari da Shettima saboda nasarorin da ya samu a ofis a matsayin daya daga cikin manyan Gwamnonin APC a kasar nan.
“Tsohon Gwamna Shettima ya iya baki kokarinsa duk da kalubalen rashin tsaro da ya fuskanta.”
A cewarsa, wannann matsalar shi ne mafi girman gwajin iyawar mutum kuma Shettima ya tabbatar da iyawarsa.
Shugaban ya tabbatar da cewa Shettima, wanda a yanzu yake yiwa mutanensa hidima a majalisar Dattawa, “bai bai wa masu kada kuri’a kunya ba saboda ya iya cika muhimman alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe.”
Shugaban kasa ya nusasshe da cewa, “daya daga cikin manyan abubuwan da za a tuna Shettima da shi shi ne yadda ya mika jihar ga wanda ya cancanta ya maye gurbinsa wato Farfesa Babagana Zulum.”