• Jam’iyar adawa ta PDP ce dai tun safari ta dakatar da Sanatan kafin ya canza sheka.
• Shugaban kasa Buhari ne ya tarbi Peter Nwaoboshi zuwa jam’iyar APC Mai Mulki.
• ym A yau juma’a ne dai Sanatan ya canja sheka inda ya bar tsohuwar jam’iyar shi zuwa APC.
Sanata Peter Nwaoboshi ya canja sheka zuwa jam’iya Mai Mulki ta APC.
An tabbatar da canza jami’iyar Sanata Nwaoboshi, wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tarbe shi, a yau juma’a, a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.
Sanatan mai wakiltar mazabar Delta ta Arewa, a jihar Delta, an ganshi a fadar gwamnatin tarayya, tare da shugaba kasa Buhari, da kuma Mataimakin Shugaban Majalissar dattijai na Kasa, wato Ovie Omo-Agege.
Inda Shugaban kasa Buhari ya tarbe shi kuma, ya tayashi murna dawowa jami’iyar APC.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kuto ta yanke wa wani dan kasuwa hukuncin zaman gidan gyaran hali na watanni18
Inda ya ce “Ina ta ya ka zuwa Ahali Mai cigaba”
Idan za a iya tunawa dai, kwanaki kadan da suka wu ce ne, jam’iyar adawa ta PDP ta dakatar da Nwaoboshi daga jam’iyar.
Inda jam’iyar PDPn ta bayyana cewa, ta dakatar da Sanatan ne, “Bisa yiwa jam’iyar zagon kasa.” Inji ta.
Comments 1