Dan takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin inuwar jam’iyyar APC Sanata Uba Sani ya kaddamar da wasu Ajujuwan karatu, a cibiyar koyar da sana’o’i a Zaria.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Sanata Uba ya tabbatar da hakan, bayan ya wallafa hotunan yadda lamarin ya kasance, a shafinsa na dandalin sada zumunta dake facebook.
Ya kara da cewa ”Na sami karramawa Bisa kaddamar da cibiyar koyar da sana’o’i, gina ajujuwa da sauran manyan ayyuka a karamar Hukumar Zaria, wanda Hon. Abbas Tajudeen (Iyan Zazzau) mai wakiltar mazabar tarayya ta Zariya a majalisar wakilai ya Samar.”
KARANTA ANAN: An Samu Sabbin Mutane 100 Da Ake Zargin Sun Kamu Da Cutar Kyandar Biri
”Irin wannan tagomashi na samar da cibiyar yana da tarin Gaida, wanda hakan zai sanya al’umma da dama su samu damar rabauta da guraben ayyukan yi musamman ga matasa.”
Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Sanata Uba Sani ya kara da cewa wannan abun arziki za su kara kaimi ga kokarin gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Nasir El-Rufa’i wajen samar da ababen more rayuwa da samar da jari ga jama’ar jihar kaduna.
Hon. Abbas Tajudeen a tsawon shekarun da suka gabata ya nuna cewa shi ne wanda ya cancanta ya cigaba da wakiltar al’ummar Zaria bisa kishinsa garesu, na samar damar sharbar roman Dimokuraɗiyya.
”Ina son na yi amfani da wannan dama wajen kira ga al’umma da kada su bijire wajen nuna goyon bayan su ga gwamnatin jihar Kaduna, sannan kuma su bayar da wannan goyon baya domin samun nasarar jam’iyyar APC a zabukan da ke tafe a jiharmu mai albarka, da ma Nijeriya baki daya,” inji Sanata Uba Sani.
Sanata Uba Sani shine Dan takarar Gwamnan jihar kaduna, Kuma Dan takarar Gwamna Mafi karfi da karbuwa duk Jam’iyun jihar.
A wani labarin kuma: Rushewar Katangar Makaranta Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Yara
Wata katanga da ta rushe a wata makaranta da ke Legas, Covenant Point Academy da ke Ajose Street, a unguwar Amukoko a jihar Legas, ya yi sanadin mutuwar yara biyu, Samat Saheed da wata yarinya da har yanzu ba a tantance ba.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa yarinyar mai shekaru tara ta wuce gaban makarantar domin tafiya inda ta nufa a unguwar yayin da Samat mai shekaru uku ke wasa a katangar makarantar, kusa da shagon mahaifiyarsa lokacin da katangar ta rushe.