Wakilin Kaduna Ta Tsakiya a Majalisar dattijan Nageriya Sanata Malam Uba Sani Ya kaddamar da katafaren dakin kwanan dalibai a Makarantar ‘yan mata ta Giwa.
A yau lahadi ne Mai Girma sanatan Kaduna ta Tsakiya Malam Uba Sani, ya kaddamar da katafaren dakin kwanan dalibai na mata a makarantar kwana ta ‘yan mata dake cikin garin Giwan jahar Kaduna, Sanatan wanda ya gina dakin mai dauke da gadaje guda 110, Yace ya gina dakin ne don kara wadata daliban da dakunan kwana.
Taron ya samu halartar Shugaban karamar hukumar ta Giwa Hon.Abubakar Shehu Lawal Giwa, tare da ‘yan majalisun jaha dana tarayya.
Daganan Sanatan ya zarce zuwa sansanin ‘yan gudun hijira dake cikin garin Iyatawa, don bayar da tallafi ga wadanda ibtila’in rashin tsaro ya korosu daga garuruwan su.
Daga karshe Mutanen Garin sunyi addu’o’i da fatan alkhairi ga Sanata Malam Uba Sani.