A daidai lokacin da wasu yan siyasa ke karkatar da akalar dukiyarsu a ɓangare na rayuwar duniya, bangaren Sanatan Kaduna ta tsakiya Uba Sani ya sha banban da na sauran, domin shi ya fi karkata ne ga tallafawa rayuwar al’umma don Kyautata gobensu.
Wannan na zuwa daidai lokacin da yake bada hankali a harkar karatun addini da malamai ke cewa na daga cikin sadaka mai gudana.
Yayin wata saukar karatun Alkur’ani mai girma da Sanatan ya hallarta a makarantar Darul Sigaril Huffaz dake Kaduna, ya bada tallafin kudi ne wuri na gugan wuri har naira miliyan ɗaya da rabi da zummar tallafa wa karatun dalibai mahaddata Alkur’ani.
Kazalika Uba Sani ya alkawarta cewa baya ga wannan tallafi, zai rika ware zunzurutun kudi har kimanin naira biliyan biyu kowace shekara don daukar nauyin karatun karin wasu dalibai ashirin a makarantar.
Sanatan ya ce la’akari da irin gagarumar gudummawa da bangaren haddar Alkur’ani ke da shi, akwai bukatar jama’a da dama su maida hankali wajen inganta shi don alkinta tarbiyar ƴaƴa masu tasowa.
Kazalika ya alakanta matsalar tsaro da Kasarnan ke fuskanta da rashin kyawun tarbiya da kuma rashin ilmin addini, inda ya ce muddin ba a tashi tsaye ba to babu shakka nan gaba za a rasa inda za a sa kai a kasarnan.
Har wa yau ya jinjina wa makarantar ta Darul Sigaril Huffaz bisa karrama shi da ta yi ta hanyar gayyatar shi wannan gagarumar sauka, inda ya sha alwashin cewa hakan taimaka matuka wajen ci gaba da hidima qa Addini.
Sanata Uba Sani dai ya yi shura wajen taimakon al’umma a bangarori daban-daban na rayuwar yau da kullum musamman matasan da ake cewa manyan gobe.