Dan takarar gwamnan jihar Kaduna a zaben 2023, Sanata Uba Sani tare da mataimakiyarsa Dakta Hadiza Balarabe sun shiryawa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na kananan hukumomi 8 na jihar taruka na musamman.
Kananan Hukumomin da suka haɗar da Lere, Ikhara, Kubau, Kudan, Makarfi, Zaria, Soba, da Sabon Gari, baki dayan su sun kasance a shiyya ta daya a jihar Kaduna.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa makasudin shirya musu tarukan shine domin daidaita dabarun yakin neman zaben, da nufin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a jihar dama kasa baki daya.
An kuma mayar da hankali a yayin taron kan warware sabanin dake tsakanin ya’yan jam’iyyar don tukarar baki daya zaben cikin hadin kai da fatan nasara.
Sanata Uba Sani ya ce ”” Ina son na yi amfani da wannan dama wajen tunatar da masu ruwa da tsaki cewa, dole ne muradin babbar jam’iyyar mu da Jihar Kaduna da Najeriya su kasance mafi girma a cikin lissafinmu.
KARANTA ANAN: Shugaban Kasa Buhari Ya Gana Da Gwamnonin Jam’iyyar APC
Dole ne mu tabbatar da haɗin kai kuma mu mai da hankali don riƙe amanar jama’a.”
Ya kara da cewa, ”Masu ruwa da tsaki sun kuduri aniyar gudanar da yakin neman zaben tallata ‘yan takarar jam’iyyar ga al’ummar jihar Kaduna.
Kuma Suna da yakinin cewa tare da hadin kai da aiki tukuru APC za tayi nasarar lashe zabe a 2023.” inji Sanata Uba sani
Sanata Uba sani Dan takarar Gwamnan jihar kaduna Karkashin jam’iyar APC shine Dan takara Mafi tasiri a duk cikin Yan takarar Jam’iyun Siyasa a Jihar ta Kaduna.
A wani labarin kuma: Kotun Kenya Za Ta Zauna Kan Batun Soke Sakamakon Zaben Kasar
Kotun kolin Kenya na shirin gudanar da wani taron share fage kan kararrakin da ke neman soke sakamakon zaben shugaban kasar. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
A makon da ya gabata ne aka gabatar da koke-koke guda tara na neman soke nasarar William Ruto.