Dan takarar gwamnan jihar Kaduna karkashin jam’iyyar APC Sanata Uba Sani, ya halarci taron tattaunawa da ‘yan takarar gwamnan jihar Kaduna wanda kungiyar The Partnership for Issues-Based Campaign in Nigeria (PICaN) tare da hadin gwiwar Legal Awareness for Nigeria Women (LANW) suka shirya a jihar Kaduna.
An kira taron ne domin tattaunawa kan mukalar kungiyoyin ‘yan kasa da tsarin ‘yan takara don cimma matsaya kan alkawurran ci gaba a muhimman sassa.
Sanata Uba ya ce taron ya ba shi dama mai kyau inda ya bayyanawa shugabannin ƙungiyoyin jama’a da masu tsara ra’ayi na guda 9 wanda aka haɗa su cikin tsanaki don magance manyan ƙalubalen ci gaban jihar Kaduna, da ci gaban da aka samu ya zuwa yanzu, da salo da aiwatar da su.
Dangane da tafiya da zamani kuwa an shirya shi ne kan wata sabuwar hanya, tare da sabbin manufofi, shirye-shirye da ayyukan da za su kai jihar zuwa matsayi mafi girma a cikin jihohin Najeriya.
A yayin taron ya amsa tambayoyi daban-daban da mahalarta wajen suka gabatar, dangane da abin da muke fatan yi ta fuskar inganta tattalin arziki, ababen more rayuwa, ilimi, lafiya da sauran fannoni.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Sanata Uba Sani ya sami damar yin karin haske kan batutuwan da aka taso da maganar su a wajen, kuma ya nuna gamsuwarsa cewa yakin neman zabe na gaba zai kasance kan batutuwa masu tsari.
”Zan yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga al’ummar Jihar Kaduna na gari, da su ba mu hadin kai a wannan tafiya tamu ta daukaka jiharmu mai daraja ta hanyar zaben jam’iyyar APC a zaben gwamna na 2023.”
Sanata Uba Sani a matsayinsa na ɗan takarar gwamna na jam’iyar APC yanzu haka na cigaba da samun karbuwa daga al’ummar jihar Kaduna.