Sanata Uba Sani ya kai ziyara ga Khalifa Muhammadu Sanusi, ya buƙaci goyon bayan sa
Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Kaduna Sanata Uba Sani ya kai ziyara ga mai Martaba Sarkin Kano na 14 Khalifa Muhammadu Sanusi, domin neman goyon baya, da shawarwari kan cigaban Jahar.
Sanata Uba sani Kuma Dan takarar Gwamnan jihar Kaduna Karkashin jam’iyar APC ne ya bayyana haka a shafinsa na Twitter, bayyana jim kaɗan bayan ya gana da Mai Martaba Sarkin Kano na 14
KARANTA WANNAN LABARIN: Sauka daga muƙami bai isa ba, HURIWA ta buƙaci a kama tsohon Alƙalin Alƙalai na Najeriya
Sanatan yace “A yau na kai ziyarar ban girma ga mai martaba Sarkin Kano na 14, Khalifa Muhammad Sanusi II”
“Tattaunawar da na yi da mashahurin masanin tattalin arziki, kuma ƙwararren masani ta kasance mai matukar fa’ida kuma mai daɗi sosai kwarai da gaske, Ina godiya ga mai martaba sarki bisa wannan karramawa” inji Sanata Uba sani.
Alamu dai tuni sun yi nuni da cewa wannan ziyara ba zata rasa nasaba ga Neman shawarar Sarkin, duba da yadda Muhammadu Sanusi lamido ya kasance tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya CBN.
“Haka Zalika yana ɗaya daga cikin masana tattalin arzikin Najeriya a kokarin Sanatan na Samar da cigaba a Jihar kaduna idan ya zama Gwamna a 2023.”
Bincike ya nuna Sanata Uba sani shine Ɗan takara Mafi kwarjini da taimakon Al’umma a zahiri a duk cikin ƴan takarar dake Neman zama Gwamnan jihar kaduna.