Sanata Uba sani mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Kuma Dan takarar Gwamnan jihar Kaduna karkashin jam’iyyar APC a zaben 2023 dake tafe, ya karyata batun da ake cewa ya gabatar da Kudiri gaban majalisa Kan kirkirar jihar Zazzau.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Sanatan ya bayyana batun a matsayin ƙanzon kurege, wanda wasu da basu son zaman lafiya suka ƙirƙirar da shi.
Da Ɗumi-Ɗumi: An Sanar Da Sakamakon Zaben Shugaban ƙasar Kenya
Sanatan ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook yana mai cewa ”Hankalina ya karkata zuwa ga wani labari karya da ke yawo a kafafen sada zumunta, cewa yanzu haka shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin kafa jihar Zazzau, wanda ake zargin na hada hannu a majalisar dattawa tare da Sanata Sulaiman Abdu Kwari.”
”Nayi mamakin yadda miyagu za su bar tunaninsu su tada tarzoma, duk da nufin lalata alakar abokin hamayyarsu na siyasa da alummarsa.”
”Ta yaya mutane za su kai ga yin shiri don tada zaune tsaye a jiharsu? da kuma ta’azzara matsalar rashin tsaro domin Sanata Uba Sani ya samu cikakken goyon bayan jama’a kuma ana ganin shi ne wanda zai sami kuri’u mafi rinjaye a zaben gwamna na 2023 a jihar Kaduna.”
”Majalisar dattawan tarayyar Najeriya ta tafi hutu, Babu irin wannan doka da ke gaban Majalisar Dattawa,” a cewar Sanata Uba Sani.
Ya kara da cewa ana gabatar da buƙatun ƙirƙirar jihohi a gaban Kwamitin Binciken Tsarin Mulki.
Don haka labarin yanzu haka yana hannun jami’an tsaro, kuma dole ne hukumomin tsaro su binciki lamarin, don gano wadanda ke da hannun a wannan Lamarin.
Ya kuma ce dole ne a gurfanar da wadanda ke da hannu a wannan aika-aika domin su zama masu hana wasu anan gaba.
”Na mai da hankali sosai ga bangarorin da suka kamata, don samar da ingantattun dabaru da nufin tabbatar da nasararmu a zaben gwamna na 2023.”
”Mun kuma yi ta raba tsarin mu na jihar Kaduna da masu ruwa da tsaki domin samun abubuwan da suka dace.”
”Tuni shirye shirye sun yi nisa don fara yaƙin neman zaɓe a watan Satumba na 2022, kuma Babu wata maƙarƙashiya da za ta iya raba hankalinmu daga manufofinmu.” inji Sanata Uba Sani.
Kawo Yanzu dai Sanata Uba sani shine Dan takara mafi samun karbuwa a wajen al’umma, cikin dukkanin yan takarar Gwamnan jihar Kaduna.