Ƴayan Jam’iyar APC na jihar Kaduna sun kuduri aniyar aiki tukuru domin ganin Jam’iyar ta lashe zaben 2023 a ko wanne mataki, a cewar Sanata Sanata Uba Sani.
Sanata Uba Sani ya tabbatar da hakan ne a lokacin zaman su na Larabar nan, wanda ya gabata tare da Shugabannin Jam’iyar APC na shiyya ta biyu a Kaduna.
KARANTA ANAN: Ganduje, Dangote, FG, Bill Da Milinda Gates Sun Cimma Wata Yarjejeniyar Fahimtar Juna
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Sanatan ya ce ”A yau, a ci gaba da taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na Kaduna domin daidaita dabarun yakin neman zabe da samar da hadin kai gabanin zabuka, ni da mataimakiyata, kuma mukaddashiyar gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Balarabe mun gana da jami’an jam’iyyarmu ta APC daga kananan hukumomi bakwai 7 da ke shiyya ta biyu 2 wanda suka hada kananan hukumomin Kaduna North, Kaduna South, Igabi, Giwa, Chikun, Birnin-Gwari da Kajuru.
Kamar yadda aka tsammata daga gare su, masu ruwa da tsakin sun kuduri aniyar tabbatar da hadin kai domin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa da na Gwamna da na Sanata da Kuma na Yan majalisar Wakilai da na ƴan majalisun Jihar Kaduna,” inji Sanata Uba Sani.
Sanata Uba sani shine Dan takarar Gwamnan jihar Kaduna Karkashin jam’iyar APC Kuma shine Dan takara mafi karfi da samun goyon bayan Al’ummar jihar a duk cikin Yan takarar Jam’iyun Siyasa dake jihar Kaduna.
A wani labarin kuma: Yayi dai-dai da Kundin tsarin mulki Shettima ya kula da Harkokin Tsaro – Fani-Kayode ga Okowa
Femi Fani-Kayode, Tsohon Ministan sufurin jiragen sama, ya ce ya dace Abokin Takarar Ɗan Takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), na shugaban kasa, Kashim Shettima, ya gudanar da harkokin tsaro idan an zabi jam’iyyar a 2023.
Fani-Kayode ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga wani tsokaci da jam’iyyar Mataimakin Dan Takarar Shugaban Ƙasa na Peoples Democratic Party, PDP, Ifeanyi Okowa, ya yi, na cewa ba bisa ka’ida ba ne Shettima ya gudanar da harkokin tsaro idan aka zaɓi APC a 2023.