Wata ƙungiya mai suna ƙungiyar jindaɗin ƙabilar Ibo mazauna Kaduna, ta bayyana goyon bayanta ga takarar gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Da yake magana a wajen wani taro a ranar Lahadi a Kaduna, lauyan ƙungiyar, Valentine Ewuzie, yace Sanata Uba Sani ya cancanta da ya ɗare kan kujerar gwamnan jihar Kaduna. Jaridar The Cable ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Bayan mun kwashe tsawon lokaci muna soyayya, saurayina ya auri wata daban -Budurwa ta koka
Ewuzie ya bayyana cewa ɗan takarar ya san mutanen ƙabilar Ibo.
“Mun duba sannan mun tantance dukkanin ƴan takarar, a yanzu haka ba tare da wata shakka ba, muna tabbatar maka da cewa kai ne ɗan takarar mu.” A cewar sa.
“Sannan a matsayin mu na waɗanda muke tsintsiya maɗaurinki ɗaya, zamu yi amfani da hakan wajen tabbatar da cewa ka zama gwamna na gaba na wannan jihar.”
Ya kuma bayyana cewa lokacin da Uba Sani yake mai baiwa gwamna Nasir El-Rufa’i shawara, ya gana da ƴan ƙabilar Ibo mazauna jihar inda ya tabbatar musu da kare lafiyar su.
Da yake magana a wajen taron, Sanata Uba Sani ya bayar da tabbacin cewa idan ya samu nasara zai naɗa ɗan ƙabilar Ibo cikin majalisar gudanarwa ta jihar.
Abun a Yaba: Sanata Uba Sani Yayi Wata Kyauta Mai Tsoka Ga Wasu Ƙungiyoyin Taimakon Al’umma
A wani labarin na daban kuma, ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna, a ƙarƙashin inuwar jami’iyyar APC, yayi wani abun a yaba.
Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC, kuma sanata mai ci a yanzu, Sanata Uba Sani, ya halarci taron ƙaddamar da bayar da gurbin karatu kyauta ga wasu daliɓai.
Taron wanda aka shirya sa domin ɗaliban makarantun tsangayoyi da kuma koyar da sana’o’in dogara da kai ga mata da matasa, ya samu halartar manyan baƙi waɗanda suka haɗa da jami’an gwamnati, sarakuna, da kuma ƴan kasuwa.