Dan takarar Gwamnan jihar Kaduna karkashin jam’iyyar APC Sanata Uba Sani na ci gaba da ziyarar samun hadin kan masu ruwa da tsaki da sauran masu fada aji a jihar, domin aiki tare da su kafin, da kuma bayan zaben 2023, idan har Allah ya bashi nasara.
Baya ga ziyartar gidan Kashim Ibrahim a yau ya samu gagarumin ci gaba na ziyartar babban mataimakin kwanturolan hukumar Kwastam mai ritaya, kuma wanda ya zo na biyu a zaben fidda gwani na APC, a jihar Kaduna, wato Alhaji Bashir Abubakar.
Sanata Uba ya ce ya yi masa alkawarin kulla alaka mai karfi tare da samar da lokacinsa da dukiyarsa don tabbatar da nasararsa a zaben 2023.
KARANTA ANAN: Babu Abunda APC Ta Haifarwa Najeriya Banda Yunwa Da Talauci – Okowa
“Ina matukar godiya ga Alhaji Abubakar bisa wannan nuna hadin kai da goyon baya domin samun nasararmu a zaben gwamna mai zuwa.”
“Wannan abin misali ne kuma dole ne a yi koyi da shi daga maza har mata na jam’iyyarmu na gaskiya kuma masu aminci, sannan da zarar an gama fafatawa a cikin jam’iyya, to dole ne mu hada kanmu, mu ci gaba da kare muradun jam’iyya da jama’armu.”
“Dole ne a ko da yaushe maslahar jama’armu ta kasance mafi girma a cikin zukatanmu.
Ina kuma so in gode wa Alhaji Abubakar bisa ga gagarumin hidima da yake yi wa Nijeriya tabbas Ya bar tabo maras gogewa a Hukumar Kwastam, kuma Kwarewar sa da basirar sa za su yi amfani yayin da muke ƙoƙarin gina kyawawan abubuwan gado na jagoranmu Gwamna Malam Nasir El-Rufai,” inji Sanata Uba Sani.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Sanata Uba Sani dai yanzu haka na ci gaba da tunbubar al’umma musamman masu ruwa da tsaki na jam’iyar duk a kokarinsa na ganin ya lashe zaben Gwamnan jihar Kaduna a zaben 2023 Mai zuwa.
A wani labarin kuma: Na Gama Nasara a Zaben 2023 Lokacin Rantsuwa Nake Jira – Dan Takarar Shugaban Kasar PRP
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PRP, Kola Abiola, ya bayyana cewa zai lashe zaben shekara mai zuwa ta hanyar maimaita irin rawar da mahaifinsa, Marigayi MKO Abiola ya yi a zaben 12 ga watan Yuni, 1993.
Kola ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a Abeokuta, ranar Asabar a wajen bikin jana’izar marigayi dan takarar gwamna na jam’iyyar PRP a jihar Ogun, Farfesa David Bamgbose.