A lokacin da yake aikewa da sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwa ga gwamnan, Sanata Uba Sani ya bayyana EL RUFA’I amatsayin wani gwamna kyauta daga Allah ga ‘yan jihar kaduna.
Sanatan ya na mai cewa “Gaisuwa ta musamman ga mai girma shugabana, mai ba ni shawara, abokina, kuma amintaccen abokin siyasa a bisa gagarumin bikin cikarsa shekaru 62 a duniya. ”
“Hakika Gwamna Nasir El-Rufai kyauta ce ta musamman ga jihar Kaduna da Najeriya; kasancewar sa mai cike da kuzari da jajircewa da kuma kawo ci gaba.” Inji Sanata Uba Sani.
“A cikin ’yan shekaru, ya mayar da Jihar Kaduna zuwa wani mataki Mai Girma da ban sha’awa. Jihar mu yanzu ta zama wata cibiyar Samar da gine-ginen zamani.”
“Yana ci gaba da magance manyan kalubalen dake damun jihar.Ya kuduri aniyar barin gadon mulkin cikin nasara tabbas na kasance mai Kima da girma da gata bisa kasancewa tare da irin wannan shugaba mai ban mamaki.”
A Karshe Sanatan ya kare da cewa, “A yayin da shugabanmu mai girma yake cika shekaru 62 a duniya, ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da yi masa jagora, ya kare shi da kuma karfafa shi.
Barka da zagayowar ranar haihuwa.