Dan takarar gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya taya Hadiza Balarabe Sabuwa murna bisa zagayowar ranar haihuwarta.
Cikin sakonsa na taya murna, Sanatan ya fara da cewa ”Albarkacin zagayowar ranar haihuwar mataimakiyar gwamnan Kaduna, Nima na bi sahun dubban jama’ar Najeriya da ma duniya baki daya, wajen taya murna ga babbar mace Mai daraja, macen da ta sadaukar da rayuwarta wajen inganta rayuwar talakawa, marasa galihu da marasa karfi a jihar Kaduna dama Najeriya baki daya.”
Ya kara da cewa mai girma Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya samu abokiyar tafiyar siyasa ta gari kuma amintacciya, abokiyar tabbatuwar kudurinsa, wajen shimfida ayyukan aikin sa na mayar da jihar Kaduna a matsayin abin koyi na cigaba a Najeriya.
KARANTA ANAN: Sabon Kwamishinan Yan Sandan Kano ya Kama Aiki
Sanata Uba Sani ya kuma Hajiya Hadiza ta yi amfani da fasaharta wajen tunkarar manyan kalubalen ci gabanta kuma ta kasance abar koyi ga mata da ‘yan mata a jihar Kaduna da ma wajenta.
”Hakika ina matukar farin ciki da samun tikitin takarar gwamna, kuma karin nasara kan hakan shine yadda na samu wannan mashahuriyar kwararriya wajen ci gaban kasa, a matsayin wadda zata yi mun mataimakiya.”
”A saboda haka insha Allah zamu yi duk mai yiwuwa wajen ganin mun ciyar da jihar Kaduna gaba, kuma fata na shine yadda zamu kai jihar Kaduna zuwa mataki na gaba, idan har munyi nasara a zaben 2023.”
”A madadin kaina da Iyalina, Ina taya Mai girma mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Murnar zagayowar ranar haihuwarta, ina rokon Allah Madaukakin Sarki Ya ci gaba da yi mata jagora, ya kare ta, ya kuma kara mata kwarin gwuiwa.”
Sanata Uba Sani wanda yanzu haka shine dan takarar gwamnan jihar kaduna a karkashin jam’iyyar APC, na cigaba da samun karbuwa ga al’ummar Jihar Kaduna, kuma kawo yanzu shine Dan takara Mafi karfi a cikin yan takarar gwamnan jihar Kaduna baki daya.
A wani labarin Kuma: EFCC Ta Kame Wasu Mutane 10 Da Ake Zargi Da Damfara Ta Yanar Gizo A Abuja
Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC shiyyar Abuja sun kama wasu mutane 10 da ake zargi da damfara ta yanar gizo.
A wata sanarwa da kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya fitar, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a wani simame da aka kai a wurare daban-daban a unguwar Kubwa da Gwarimpa a Abuja bisa zarginsu da hannu wajen damfarar yanar gizo.