Ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar APC a jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya halarci wajen horas da malaman addinin Musulunci da limamai, wanda cibiyar bunkasa zaman lafiya, bincike da ci gaban Musulunci ta shirya.
A yayin ganawarsa da manema labarai, Sanata Uba Sani ya yabawa wadanda suka shirya taron horaswar, a cewarsa wannan hangen nesa ne matuka a kokarin tabbatar da zaman lafiya, da kuma ci gaban addinin musulunci.
Daga nan sai yayi amfani da wannan damar wajen kira ga wadanda suka amfana da horon, kan su koma zuwa yankunan tare da aiwatar da abinda suka koya a aikace, wanda yake fatan zai taimaka wajen samar da hadin kai da zaman lafiya mai dorewa.
Baya ga wannan taron horaswar, Sanata Uba Sani ya kuma halarci taron Fityanul Islam, wanda shima ya samu halartar manyan malamai daga sassa daban daban na jihar Kaduna.
A cewar Sanata Uba, taruka irin wadannan da ake samun wasu masu hangen nesa na shiryawa abun yabawa ne, domin kuwa zai bada damar kafa Mu’amala kyakkyawa a tsakanin al’ummar musulmi.
Wannan dai na daga cikin abunda Sanatan ya fi mayar da hankali akai, kuma ya jaddada cewa matsawar yayi nasarar zama gwamnan jihar Kaduna a 2023, zai dora kan wadannan abubuwan alkhairi.
Sanata Uba Sani dai yanzu haka shine ɗan takara mafi karɓuwa a cikin yan takarar gwamnan jihar Kaduna, kuma al’umma kullum tururuwar zuwa suke domin marawa tafiyarsa baya.