Sanata Uba Sani Ya Yi Gana Da Dagattai Da Limamai, Ya Buƙaci A Zaɓi APC
Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Kaduna a karkashin Jam’iyyar APC Sanata Uba Sani ya yi taro da Dagattai, da Limamai da sauran manyan Maluman addinin musulunci a karamar hukumar Igabi.
Sanata Uba Sani ya yi kira ga Malaman da su faɗakar da mabiya addinin musulunci domin su zaɓi Jamiyyar APC a zaɓen Shugaban Ƙasa, dana Gwamna da Ƴan Majalisun Dattawa da Majalisar wakilai, sa ƴan majalisun jiha.
KARANTA WANNAN LABARIN: Maiduguri: Yadda Dubban Jama’a Suka Yi Wa Taron Gangamin Tinubu Da Shettima
Taron dai na daga cikin wata dabara ta neman ƙuri’un al’umma tun daga matakin farko, wanda shi ya sanya ya kira taron da Maluman Addini.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na Facebook, da Jaridar Dimukuradiyya ta samu.
Ya rubuta “A ci gaba da gudanar da yakin neman zabe gabanin zabuka, na yi ganawa da Dagattai, da kuma Limamai da Malamai daga karamar hukumar Igabi. Na kuma bukace su da su fito tare da karfafa wa mabiyansu kwarin guiwa da su zabi babbar jam’iyyar mu ta APC a zaben shugaban kasa da na Gwamna da na Sanata da na Majalisar Wakilai da na Jiha”