Sanatan ne ya sanar da labarin a Yau juma’a ya na bayyana cewa, ire iren Farin Ciki daya shiga da samun wannan nasara a majalisar ta dattijan Nageriya, Sanatan na Cewa.
“Na yi matukar farin ciki samun labarin cewa, na Kasance na samu matsayi lamba na 1 a cikin Manyan Sanatocin da Suka gabatar da kudrin ci gaban doka wato (productivity index) wanda babban Kwamitin Kula da Dokoki da Ƙungiyoyin Ba da Shawara ta kasa , ORDERPAPER NIGERIA ta fitar, a farkon zama na majalisa.
Sanatan ya Kara da cewa, “Na yi alkawari ga mazabata da ‘yan Najeriya cewa, zan ci gaba da kawo alkhari tare da kafa Tarihi wajen Samar da sabbin Ayyuka Matukar Ina raye, domin rayuwar Jama’ar wadanda suka dauki nauyin na tare da bani yardarsu zan ci gaba da tallafawa tare da kuma daukar nauyin wa’yan nan kudrin, doka masu mahimmanci da ci gaban da za suyi tasiri ga ‘yan Kaduna ta Tsakiya da Najeriya gaba ɗaya. Tabbas Ina jin gamsuwa cewa ya zuwa yanzu a Kan Ayyukan Dana gabatar ga Al’umma ta Amma Duk da haka ba zan samu hutu ba zan ƙara ƙoƙari domin yi wa mutanena hidimar gaske Ina godiya ga duk wanda ya ba da gudummawa ga wannan gagarumar rawar da na taka” Inji Sanatan