A jiya Lahadi, Wani dan majalisar dattawa na jam’iyyar APC mai mulki, Sani Musa, ya yi kira ga mai bawa Shugaban Kasa shawara akan harkokin tsaro Babagana Monguno da ya yi murabus a matsayin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA).
Sanata Musa wanda ya fito daga Nijar – daya daga cikin jihohin da hare-haren ‘yan ta’adda suka fi ta azzara ya yi tir da tabarbarewar yanayin tsaro a fadin kasar nana.
Ya yi imanin Monguno, Manjo Janar mai ritaya kuma tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasa, ba shi da wani dalilin da zai sa ya ci gaba da zama a matsayin babban mai tsare-tsare kan harkokin tsaron Najeriya yayin da ake ci gaba da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Kafar yada labarai ta Channels TV ta ruwaito cewa, masu dauke da makamai wadanda ba jami’an gwamnati ba ne, da suka hada da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda, sun kara kaimi a baya-bayan nan, inda suka kara kai hare-hare kan jami’an tsaro kamar gidan gyaran hali da ke Abuja da wasu jami’an tsaro a sassan kasar nan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwamitin Majalisar Dattawa Ya Yabawa NAF Bisa Tura Jiragen Super Tucano
Daya daga cikin irin wannan harin shi ne harin da aka kai wa dakarun rundunar tsaron fadar shugaban kasa da ke bada tsaro ga fadar gwamnatin tarayya da kuma babban birnin Tarayya Abuja, inda aka ce an kashe wasu sojoji a gayin harin.
A wani labarin kuma na daban.
Biyo bayan barazanar da wasu kungiyoyin ta’addaci suka yi na kaiwa wasu manyan biranen Najeriya hare-hare a jiya, rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta bayyana cewa ta tsaurara matakan tsaro a kusa da wuraren da ake gudanar da ibada da wuraren shakatawa a fadin jihar.
Dangane da barazanar harin ta’addancin da aka shirya kaiwa manyan biranen kasar nan da suka hada da Legas da Kuma babban birnin tarayya Abuja Wanda ya karade shafukan sada zumunta na zamani.
Idan za a iya tunawa, a cikin makon da ya gabata, ‘yan ta’adda sun kai hare-hare da dama a wasu unguwannin dake cikin birnin tarayya Abuja, inda suka yi ta kashewa tare da yin awon gaba da wasu da dama a lokacin faruwar farmakin.
Sai dai kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Legas, Abiodun Alabi, ya ce an sanya hukumar leken asiri ta jihar (SIB) da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana.
Alabi, ya Kara da cewa rundunar na aiki tare da sauran jami’an tsaro domin samar da tsaro a fadin jihar, tare da ba mazaunan Legas tabbacin yin sana’arsu ta yau da kullun ba tare da wata fargaba ba.
A karshe ya umurci mazauna jihar Legas da su kasance cikin taka-tsan-tsan tare da kai rahoton duk wani motsi akan duk wasu mutane da suke zargi ga hukumomin tsaro ba tare da bata lokaci ba.