Majalisar dattawa ta yi kira ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya jagoranci gwamnatin tarayya wajen bayyana sunayen shugabannin ‘yan ta’adda a matsayin wadanda ake nema ruwa a jallo.
Majalisar ta yi wannan kiran ne a yau Laraba a wani kuduri mai kunshe da abubuwa shida da majalisar ta cimma, biyo bayan wani kudiri da aka yi la’akari da shi kan bukatar gaggauta kawo karshen matsalar satar mutane da rashin tsaro a sassan kasar nan.
Kudirin mai taken, “Bukatar gaggawar shawo kan duk wani nau’in garkuwa da mutane, ‘yan fashi da matsalolin tsaro d Suka shafi kananan hukumomin Wasagu-Danko, Sakaba, da Yauri a Jihar Kebbi”.
Sanata Bala Ibn Na’allah (Kebbi ta Kudu) ne ya dauki nauyin gabatar da kudurin, yayin da Wasu Sanatoci 12 suka mara Masa baya, a cewar wata sanarwa da Dokta Ezrel Tabiowo, mataimaki na musamman ga Shugaban Majalisar Dattawa.
Na’allah, a nasa jawabin, ya nuna damuwa da yadda matsalar tsaro ke karuwa a kananan hukumomin Danko/Wasagu da Sakaba na jihar Kebbi da ma fadin tarayyar Najeriya.
A cewarsa, ‘yan bindigar suna ta yawo cikin daruruwan mutane daga kauye zuwa kauye, gida gida suna neman shanu domin yin sata da kuma sace mutane, hakan ya Sanya su ke fatan ganin komai ya kawo karshe.