Yayin da Majalisar Dattawa ta koma zamanta a ranar Talata, Sanatoci sun yi Gum kan korafe-korafen su na tsige shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Sanatocin daga jam’iyyun adawa irin su PDP, NNPP, Labour Party, All Progressives Grand Alliance, Youth Progressives Party, da wasu takwarorinsu na jam’iyyar APC mai mulki, sun ci gaba da bayyana takaicinsu kan matsalar tsaron Najeriya.
Matsalar tsaro da ke kara tabarbarewa, ta sanya Sanatocin barazanar tsige Shugaban kasar kafin hutun makonni shida.
To sai dai bayan da aka koma zaman, babu daya daga cikin Sanatocin da ya tabo batun ko kuma yi wa manema labarai karin haske bayan ganawar tasu ta sirri.
KARANTA ANAN: Magoya Bayan Bola Tinubu, Sun Yabawa Sanata Uba Sani Kan Tafiya Da Mata A Harkar Mulki
A maimakon haka, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya yiwa mambobin zauren Barka da dawowa daga hutun da suka tafi.
Kafin a fara zaman, bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor-Kalu, ya shaida wa manema labarai cewa matakin ya ci tura.
Kalu, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa wasu daga cikin tambayoyi daga manema labarai, ya ce ko da an dauki irin wannan mataki a yanzu, za a yi watsi da shi, domin a halin yanzu yawancin Sanatoci na bayan Shugaban kasa.
A wani labarin kuma: Yajin Aikin ASUU: NANS Zata Tare Hanyar Filayen Jiragen Saman Abuja/Kaduna
Kungiyar daliban Najeriya ta kasa ta ce mambobinta za su tare hanyar filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikwe, dake Abuja da kuma filin jirgin sama na Kaduna a yau Laraba.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa zasu dauki wannan mataki ne a wani bangare na zanga-zangar nuna adawa da matakin da kungiyar malaman jami’o’i ke yi.
A ranar Litinin din da ta gabata daliban sun tare hanyoyin shiga filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Ikeja, inda fasinjojin jirgin da sauran su suka gamu da tsaiko.