Gwamnan Jahar Lagos Babajide Sanwa-Olu ya amince da rage kuɗaɗen da ake karɓa ga waɗanda suka karya dokokin hanya a jahar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Gwamnatin Jahar ta fitar a ranar Talata.
Acewar sanarwar, Gwamnan ya gana da wasu da suka karya dokokin hanya, a lokacin da yakai masu ziyarar ba zata a inda ake riƙe da ababen hawan su dake Alausa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Anambara: Fashewar lskar Gas Ta Kashe Dalibar Jami’ar UNIZIK
Dalilin ziyarar shine a duba yadda ake gudanar da aikace-aikace a sashen.
Wasu da suka karya dokokin hanyar sun buƙaci Gwamnan daya shiga lamarin domin su samu sauƙi.
Duk da sun karya dokar, Gwamnan ya amince da a rage masu tara akan laifin da suka aikata.
Sanarwar ta naƙalto Sanwa-Olu na cewa “duk kun karya dokokin hanya, kuma yanzu kuna anan, domin kai ku kotun tafida gidan ka sakamakon laifuffukan da kuka aikata.
“Na ɓukaci a bani jerin sunayen ababen hawan dake wuraren, kuma zan gana da masu kula da karya dokokin hanya.
“Zamu ga wane hukunci ya kamata mu yanke akan laifin ku, domin ganin an rage kuɗaɗen da zaku biya.
Comments 1