Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, ya gabatar da sandar mulki da kayan aiki ga HRM, Oba Abiodun Muslim Ogunbo na Ogudu Oshadi na masarautar Ogombo a Eti-Osa ta Gabas dake jihar.
Sanwo-Olu wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin kananan hukumomi da masarautu; Hon. Bolaji Kayode Robert, ya ce iyayen sarauta sun kasance abokan huldar gwamnati saboda irin rawar da suke takawa a matsayin wakilai na ci gaba, masu samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin dukkan mutane da mazauna yankinsu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kano Zata Hada Kai Da UNICEF Don Duba Yadda Ake Bayan Gida A Fili Barkatai
Gwamnan ya ba da tabbacin gwamnatin jihar za ta ci gaba da hada kai da sarakunan jihar tare da tabbatar da ganin an biya musu bukatunsu yadda ya kamata, duk da cewa ya yi murna da sarkin da ya hau karagar mulki a matsayin sarki na farko a cikin al’ummar.
Ya ce zabin da sarakunan suka yi da kuma karbuwar da al’ummarsa suka yi na jagorantarsu da kuma zama mai kula da al’adun masarautar, hakan ya nuna amincewarsu da suke da ita na iya yin tasiri mai kyau ga arzikin kasa da al’ummarta. .
“A madadin kaina, gwamnati da al’ummar Jihar Legas, ina taya mai martaba Sarki murnar hawa kujerar. Zabarku da Sarakuna da kuma karbuwar da jama’arku suka yi na jagorantarsu da zama masu kula da al’adun wannan Masarautar alama ce ta amincewarsu kan iyawar ku ta yin tasiri mai kyau a cikin wannan fili da al’ummarta.
Sabon Sarki mai jiran gado, Oba Abiodun Ogunbo, ya bada tabbacin cewa mulkin sa zai tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’ummar Legas.
Ogunbo ya zama sarki na farko a cikin al’ummar tun lokacin da aka kafa ta a ranar 4 ga watan Oktobar shekarar 1873. Kafin hawansa sarauta jiya, shi ne mai rike da sarautar Baale na al’ummar.
“Ina taya daukacin ‘yan kabilar Ogombo murnar wannan lokaci na tarihi. Tun daga ubannimmu har zuwa samarinmu da uwayenmu, da hakan ba zai yiwu ba in ba tare da addu’o’insu da goyon bayansu ba, musamman sadaukarwa.
“Ina kuma godiya ga iyalina don suna tare da ni a tsawon lokaci da kuma kasancewa ginshiƙi na goyon bayan ɗabi’a.
“Muna jinjina wa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu. Muna godiya ga majalisar zartarwa saboda ganin mun cancanci sarauta tare da sanya gwagwarmayarmu ta zama mafarki. Ina taya ‘ya’yan Ogombo maza da mata murna.”
Shima da yake jawabi, babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi da jindadin al’umma ta jihar Legas, Kikelomo Sanyaolu, ya ce: “Ina taya mutanen Ogombo murna saboda wannan abu ne mai cike da tarihi ganin cewa wannan shi ne karon farko da al’ummar Ogombo za su samu sarki.
“Ina kira ga mutanen Ogombo da su taimaka wa Oba, duk wasu bukatu na gwamnatin jihar kuma ma’aikatar shari’a ta wanke shi kuma ta same shi da cancantar mukamin. Don haka muna kira da a tallafa masa domin ci gaban al’umma . Ina da tabbacin cewa zai kai al’umma wurare.”
A yayin da yake yin alkawarin bayar da tallafi, mambobin mazabar Eti-Osa 1, Noheem Adams sun kuma yi kira ga al’umma da su yi aiki tare da sarkin.