By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, yace za a samar da rukunin gidaje 3,400 ga ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu domin samun damar mallakar gidajen.
Sanwo-Olu ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake kaddamar da shirin bayar da jinginar gidaje a Legas, a Ibeshe dake Ikorodu.
Sannan yaci gaba da cewa, “A bisa tsarin da muke da shi na hada kai da kuma sadaukar da kai ga jin dadin ma’aikata, ina mai farin cikin sanar da mu cewa muna samar da wani tsari na musamman ga ma’aikata a jihar.
“Ma’aikata su ne man dake sanya wa injin ci gaba a jihar. Mafi kyawun abin da zamu iya yi don mayar da gudummawar da suke bayarwa ga al’ummarmu shine inganta hanyarsu ta mallakar gida.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa gwamnan yace “Nan bada jimawa ba gwamnatin jihar zata kammala wani shiri da wani mai zaman kansa wanda zai gina jimillar gidaje 3,400 ga ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar.
Kazalika yace “Za a gina tsarin da aka fi sani da)(Imota Workers City) a kan fili mai fadin hekta 20 a Imota. Ma’aikata a cikin jama’a da masu zaman kansu zasu shiga cikin rukunin gidajen a kan tsarin jinginar gida mai dacewa wanda ya wuce shekaru 15 tare da adadin riba guda ɗaya.”
Kwamishinan gidaje, Moruf Akinderu-Fatai, ya bayyana cewa gwamnati zata kammala dukkan gidajen da gwamnatocin da suka gabata basu kammala ba, inji shi.
Comments 2