By Abbas Yakubu Yaura
Sarakuna a jihar Imo sun shiga buya sakamakon yawaitar kashe-kashe da sace-sacen abokan aikinsu a jihar.
Kamar dai a kidayar baya, an kashe sarakunan gargajiya akalla biyar tare da yin garkuwa da wasu da dama.
Rikicin kan sarakunan gargajiya ya fara ne a ranar 7 ga watan Afrilu lokacin da wasu ‘yan bindiga suka sace Eze Charles Irogebu na al’ummar Umuezie dake karamar hukumar Nguru-Aboh Mbaise tare da wasu hakiman majalisarsa.
Sarkin da aka sako kwanaki bayan ya koma fadar sa ne bayan halartar wani daurin auren gargajiya da aka yi a karamar hukumar Ehime Mbano inda masu garkuwa da mutanen suka tsallaka ayarin motocinsa biyu suka yi awon gaba da shi da shugabannin majalisar ministocinsa.
Eze E. Durueburuo na yankin Okwudor mai cin gashin kansa da Sampson Osunwa na yankin Ihebinowerre mai cin gashin kansa, dukkansu a karamar hukumar Njaba ta jihar sun gamu da ajalinsu ne a ranar 19 ga watan Oktoba yayin da suke ganawa da shugaban kwamitin riko na yankin. Yayin da sarakunan gargajiyan biyu suka mutu nan take, wasu biyu kuma sun shiga cikin suma, inda kuma aka garzaya dasu wani asibiti da ba a bayyana ba inda aka farfado dasu.
A wannan rana, basaraken gargajiya na yankin Etekwuru mai cin gashin kansa a karamar hukumar Ohaji-Egbema, Kenneth Okereke, ya tsallake rijiya da baya, yayin da maharan suka yi masa luguden wuta a fadarsa da motar jami’an tsaro bayan ya tsere.
A ranar 19 ga watan Nuwamba, an yi garkuwa da basaraken gargajiya na Achi Mbieri a karamar hukumar Mbaitoli, Henry Madumere, a Iho a karamar hukumar Ikeduru a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa wani taron jama’a.
Basaraken octogenarian wanda shine mahaifin tsohon mataimakin gwamnan jihar, Eze Madumere, an sako shi daga hannun wadanda suka sace shi bayan kwanaki shida.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A wani lamari na baya-bayan nan, a ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da basaraken gargajiya na tsohuwar masarautar Umuezeala-Ama dake karamar hukumar Ehime Mbano a jihar Imo.
A ranar Lahadin data gabata ne aka yi garkuwa da wasu sarakunan gargajiya guda biyu, Acho Ndukwe da Paul Ogbu tare da lalata gidajensu.
Yayin da aka ceto Ndukwe bayan awanni 24,sai kuma an ga gawar Ogbu inda aka jefar da ita.
Lamarin dai ya tilastawa galibin sarakunan gargajiya shiga buya inda wasu suka yi hijira tare dayin watsi da fadarta su.sai dai tuni wasu daga cikinsu suka dai kwana a fadarsu yayin da kuma suka yi yunkurin karfafa jami’an tsaro.
Daya daga cikin masu rike da masarautun gargajiya daya zanta da wakilinmu cikin aminci, ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda ake ci gaba da kai hare-hare a cibiyar gargajiya a jihar.inda yace sun dogara ne kawai dayin addu’o’in neman taimakon Allah.
Da aka tambaye shi ko menene zai iya zama sanadin hakan, sai yace, “Ban sani ba.Watakila suna ganinmu a matsayin wani bangare na matsalolin da kasar ke fama dasu. Amma wannan ba daidai ba ne. Basaraken gargajiya a Imo yana karbar Naira 87,000 a matsayin alawus yayin da a Arewa masarautu ke da nasu kasafin kudin, Wannan bai isa ya kashe mu ba. Amma abin da zan iya cewa shi ne, wasu dakaru masu tayar da hankali suna fakewa a halin da ake ciki yanzu don sasanta da yawa”.