Sarauniya Elizabeth II: Buhari ya bada umarnin maido da Tutocin Najeriya ƙasa-ƙasa
Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin sausauto da dukkanin tutoci a ƙasar nan da ofisoshin jakadanci na ƙasashen Ƙetare a ranakun 11 da 12 ga watan Satumba domin girmama rasuwar Sarauniya Elizabeth ta biyu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matsafa sun hallaka wata Ƙaramar Yarinya a Jihar Filato
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.
“Muna miƙa saƙon ta’aziyyar mu ga Gwamnati da Mutanen Burtaniya da duk waɗanda abin ya shafa na Ƙungiyar Kula da Tattalin Arziki ta Duniya da kuma al’ummar Duniya baki ɗaya.
“Sarauniya ta mutu, ran Sarki ya dade,” in ji shi.
A wani labarin kuma: Kaduna 2023: NNPP ta maka INEC Kotu, ta buƙaci soke Takarar Uba Sani
Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) reshen Jihar Kaduna ta maka Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) Kotu.
Tana neman a soke Sanata Uba Sani dan takarar gwamna na jam’iyyar APC bisa zargin tafka magudi a zaben fidda gwani da aka gudanar a ranar 27 ga watan Mayun 2022.