Miss Nyekachi Douglas ta lashe gasar zama Sarauniyar kyau ta Nijeriya a gasar da aka shirya na shekararnan ta zama wacce ta fi kowa kyau a Nijeriya ta shekarar 2019 wanda ya gudana a cibiyar al’adu ta Gabriel Okara a jihar Bayelsa.
Miss Nyekachi ta yi nasara ne kan mutum 36 wadanda suka shiga gasar ta zama wadanda suka fi kowa kyau a Nijeriya. Sannan ta lashe kyautar “Miss Amity.”
Gasar na MBGN pageant, an fara shi ne a cikin shekarar 1983, wanda kafin a sauya wa gasar suna, sunan gasar ‘Miss Universe Nigeria.’ Inda bayan gasar ya fara samun hadin kan al’umma, a cikin shekarar 1986 aka sauya masa suna zuwa ‘Most Beautiful Girl in Nigeria.’