Sarkin Biritaniya, Sarki Charles III ya tashi zuwa Scotland washegarin bikin jana’izar mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth II.
Ya bar filin jirgin saman Aberdeen a yau Talata bayan ya tashi daga RAF Northolt a yammacin London.
An yi imanin shi da Sarauniya Consort Camilla sun tashi zuwa Scotland don yin wasu bukatu na kashin kai.
KARANTA ANAN: Da Yawan Dalibai Wasu Sun Yi Ciki, Wasu Kanikanci – NANS
A jiya, an binne Sarauniya Elizabeth kusa da Yarima Philip a St George’s Chapel dake Windsor.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa dangin sarauta na sake yin wani mako na makoki bayan jana’izar a ranar Litinin.
Sarauniyar, wacce ita ce mafi dadewa a tarihin Biritaniya, ta mutu a Balmoral a ranar 8 ga Satumba.
A wani labarin kuma: Abba Gida Gida Ya Magantu Kan Wani Faifan Bidiyo
Dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar (NNPP), Abba Kabir Yusuf, ya nesanta kansa daga wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta na yanar gizo yana mai cewa ya amince da wasu tarin kudin da aka tara masa, inda kowa ya bayar da naira 1,000 daga wasu masu sha’awa da kuma ‘yan majalisar tarayya.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, dan takarar gwamnan ya bukaci al’ummar Kano musamman ‘yan jam’iyyar NNPP da su yi watsi da faifan bidiyon.