Sarki Charles na uku ya ki amincewa da bukatar shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa na halartar jana’izar Sarauniya Elizabeth ta biyu.
A baya dai Mnangagwa a cikin wata wasikar ta’aziyya da ya aikewa sarkin ya bukaci halartar jana’izar Sarauniyar duk da cewa ba a saka shi cikin jerin shugabannin kasashen duniya da fadar Buckingham ta gayyace su zuwa jana’izar ba.
KATANTA WANNAN LABARIN: Mutane Na Tserewa Yayin Da Harsashin Soji Ya Sami Mutum Biyu
Sarkin, a cikin wata sanarwa da mataimakiyar babban jami’in yada labaran sa, Miss Jennie Vine, fitar a ranar Asabar kuma Jaridar PUNCH ta ce ta samu, ya bayyana cewa, an ki amincewa da bukatar shugaban kasar Zimbabwe kan rahotannin take hakkin dan Adam a kasarsa.
Sanarwar ta kara da cewa, “Mai martaba Sarki Charles III, ya bukaci in sanar da ku cewa ba za a iya amincewa da bukatar shugaba Mnangagwa ba, domin hakan zai sabawa dokar hana zirga-zirgar da Birtaniya ta yi wa wasu da dama.”
“Shugabancin gwamnatin Zimbabwe da wadanda ke da alaka da su.”
“Har ila yau, akwai damuwa kan rahotannin da aka tabbatar na rashin mutunta hakkin dan Adam da ke faruwa a Zimbabwe.”
“Kamar yadda kuka bayyana a cikin ƙarin wasiƙar ku, an gayyaci sauran shugabannin duniya, ciki har da na Afirka, kuma mun lura da damuwar ku cewa ba a gayyaci shugaba Mnangagwa ba don kyakkyawar dangantakar ƙasa da ƙasa kuna ganin ya kamata ya kasance, duk da haka har yanzu takunkumin da aka sanya masa na aiki
A WANI LABARIN KUMA: EFCC Ta Kama Masu Damfara Ta Yanar Gizo A Jihar Kwara
Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) na shiyyar Ilorin sun kama mutane 16 bisa zarginsu da aikata laifuka ta yanar gizo da kuma mallakar makudan kudade ba bisa ka’ida ba a Ilorin, jihar Kwara.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren, ya fitar a ranar Juma’a, ta ce an kama su ne a ranar Alhamis, biyo bayan sahihan bayanan sirri da hukumar ta gudanar.