Daga Abbas Yakubu Yaura
Sarkin Kwatarkwashi da ke karamar hukumar Bungudu, wanda ya fi kowa dadewa kan karagar mulki a jihar Zamfara, Alhaji Ahmad Umar (Mai-Kwatarkwashi), ya rasu ne a ranar Alhamis yana da shekaru 93 a duniya.
Kafin rasuwar Sarkin dai ya shafe shekaru 61 a kan karagar mulki.
Sakataren gwamnatin jihar Kabiru Balarabe, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, ya ce sarkin ya rasu ne bayan ya sha fama da doguwar jinya yana da shekaru 93.
Mista Balarabe ya ce an gudanar da sallar jana’izarsa da karfe 6:30 na yamma a garin Kwatarkwashi mai tarihi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Idan zaku iya tunawa Sarkin Musulmi Abubakar III ya nada Mai Kwatarkwashi sarauta a ranar 17 ga watan Maris shekarar 1961, kuma ya rasu a fadarsa.
Har zuwa rasuwarsa, shi ne sarki mafi girma a jihar Zamfara wanda ya shafe shekaru 61 akan karagar mulki.
NAN
A WANI LABARIN KUMA
Harin Cocin Owo: An kama wasu da ake zargin a Ondo
An kama wasu da ake zargin sune suka kai hari cocin Katolika ta St. Francis Catholic Church da ke Owo, a jihar Ondo.
Wani faifan bidiyo da ya karade kafafan sada zumunta na zamani ya nuna yadda jama’a ke zanga-zanga a cikin fadar Olowo na Owo, Oba Ajibade Ogunoye.
Ana iya jin daya daga cikinsu yana cewa: “Suna so su kai su Akure ( wadanda ake zargin). Matasan sun fusata.”
A ranar Lahadin da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki cocin tare da kashe wasu masu ibada da suka hada da mata da kananan yara a Ondo.
Adadin wadanda suka mutu ya kai 40, yayin da wasu kuma suka samu raunuka a asibiti suna karbar kulawa.
Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa, wasu daga cikin maharan sun yi shigar burtu a matsayin gungun jama’a na masu ibada, kuma sun yi ta harbi da bindigu kirarAK-47.
Hukumar tsaron ta kuma sanar da cewa an gano wasu bama-bamai guda uku da ba su tashi ba a wurin.
Comments 1