Mai martaba Sarkin Argungu Alhaji Sumila Mera a ranar Lahadi ya naɗa Ministan Yaɗa labaru da Al’adu na Ƙasa Lai Mohammed a matsayin Kakakin Kebbi, ma’ana wakilin al’adar Kebbi.
Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa ya bada rahoton cewa naɗa sarautar wadda ta faru a a fadar mai martaba sarkin Argungu dake Argungu a jahar Kebbi, na daga cikin murnar ranar yawon buɗe ido ta duniya, da akayi bikin murnar zagayowar ta a Birnin-Kebbi a ranar Litinin.
Dayake jawabi a lokacin taron, Sarkin yace an baiwa ministan sarautar sakamakon ƙarfin gwuiwa da yake dashi wajen cigaban al’adun ƙasa ya zuwa matakin duniya, kamar yadda majiyar jaridar Dimokuraɗiyyar ta ruwaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya ta bukaci Derebobin Manyan motoci da su fahimci halin da ake ciki
Mai martaba sarkin yace masarautar ta girmama ministan da sarautar a matsayin godiya ga ƙoƙarin shi, na inganta harkokin al’adu a lokacin bikin baje kolin al’adu da kama kifi na Argungu, domin ya zama dai-dai da duniya.
Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa ya ruwaito cewar, bikin Argungu ya samu halartar baƙi daga gida da wajen ƙasar.
Sarkin ya kuma yabawa Ministocin yaɗa labaru da suka wuce a ƙoƙarin su na inganta harkokin al’adu a ƙasar tun shekarar 1970.
“A madadin al’ummar masarautar ina yi maka barka da zuwa, kuma muna baka tabbacin cewa, zamu riƙa sanya ka a dukkanin abun da ya shafi masarautar,”inji shi.
Uban Ƙasar ya buƙaci ministan daya amshi karamcin ta hanyar cigaba da inganta harkokin al’adu a Kebbi da Masarautar Argungu gaba ɗaya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu jiga-jigan APC da magoya baya, sun koma jami’iyyar PDP a Gombe
Ya bada tabbacin cewa masarautar da ƙasa zasu cigaba da amfana da ɗumbin ilmi da Ministan ke gareshi.
Ministan ya godema Sarkin da Al’ummar Argungu gaba ɗaya da soyayyar da suka nuna mashi, musamman wajen girmama shi da suka yi ta hanyar bashi Sarautar.