Mai Martaba Sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Suleiman Adamu ya karrama tsohon Shugaban kasar nan Goodluck Ebele Jonathan da wata gagarumar sarauta ta Jigon Bauchi.
A yau talata ne Sarkin na Bauchi ya nada Jonathan bayan da ya kai wata ziyarar kaddamar da ayyukan raya al’umma da Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya gayyace shi izuwa fadar gwamnatin jihar bauchi.
Wannan nadi a cewar Dakta Rilwanu suleimanu Adamu na zuwa ne la’akari da irin namijin kokarin tsohon shugaban kasar wajen gina kasar nan.
Da yake jawabi tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ya yaba wa Sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Suleimanu Adamu bisa wannan karamci inda a lokaci gguda ya alkawarta cewa zai yi aiki tukuru wajen ci gaba da hada kan alummar kasar nan.
Wannan sarauta dai ta janyo cece kuce tsakanin al’ummar kasarnan inda wasu ke ganin chanchantar hakan yayin da wasu kuma ke nuna shakku kan chanchantar ta.
Wakilin mu Bashir Khalid Furyam wanda ya kasance a gurin taqron ya labarto mana cewa dubun-dubantan jama’a ne suka yi dandazo don nuna mubaya’ar su ga tsohon shugaban kasar.
Kuma wannan ziyara ta tsohon shugaban kasar tana zuwa yayin da ake tsaka da yamadidin cewa akwai yiwuwar ya tsaya takarar shugabancin kasa karkashin inuwar Jam’iyyar APC wacce ta sha banban da ta Gwamnan Jihar Bauchi din.