A ranar Laraba ne Sarkin Fulanin Kano na 14, Malam Muhammadu Sanusi II ya ziyarci tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa rasuwar kaninsa, Kwamared Inuwa Musa Kwankwaso.
Dimokuradiyya ta ruwaito cewa Kwamared Inuwa Musa Kwankwaso ya rasu ne a ranar 20 ga Disamba, 2021 a asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH) bayan ya sha fama da jinya.
Khalifa Muhammadu Sanusi II, wanda shi ne shugaban Darikar Tijjaniyya a Najeriya ya kai wa Sanata Rabi’u Kwankwaso ziyarar ta’aziyya a Abuja.
Ya bukace shi da ya hakuri da hukuncin Allah a matsayinsa na mai bayarwa da kuma karbar rayuwa.
Da yake mayar da martani, Sanata Kwankwaso ya yabawa Malam Muhammadu Sanusi II bisa ziyarar da kuma wadanda suka raka shi.