Sarkin Ibadan ya maida jawabi, kan Allah wadai da Igboho yayi na bada Sarautu ga Ganduje, Matar shi
Olubadan na Kasar Ibadan, Oba Lekan Balogun a ranar Litinin yace Ɗan Gwagwarmayar neman Kafa Ƙasar Biafra Sunday Igboho dole yasan cewa, wasu ma suna da damar suyi abinda suka ga ya dace, kuma zai kawo wa Ƙasar Yarbawa cigaba.
Olubadan ya maida jawabi ne akan wani bidiyo na Ɗan Gwagwarmayar Yarbawa Sunday Adeyemo, da aka fi sani Sunday Igboho yana Allah wadai da bada sarautun gargajiya ga Gwamnan Jahar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da Matar sa, Farfesa Hafsat Umar Ganduje.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abuja: Musa Ɗan Shekara 16 shiya koya man neman Maza — Cewar Matashi Mai shekaru 36
A cikin bidiyon da aka haska a Fadar Olugbon na Orile-Igbon, Oba Francis Olusola Alao, an ga Sunday Igboho yana baiwa Sarkin Shawara akan kada bi sahun wasu Sarakunan Yarbawa wajen bada sarauta ga mutanen da basu yi wani abun kirki a gare su, kuma ya shawarci Olugbon ya shawarci Sarakunan dasu daina hakan.
Da yake maida jawabi akan Maganganu ga Olubadan da akayi a harshen Yarbanci, Mai Magana da Yawun Fadar Oladele Ogunsola duk da dai babu wani suna da aka kama a bidiyo, amma yace Lamarin da ya faru a ranar Asabar abun a yaba ne.
“Mutumen da aka baiwa Sarauta (Gwamna Ganduje) yana da Son Yarbawa, domin a halin yanzu yana gina ɗakin Karatu mai girma a Jami’ar Ibadan, inda yayi Digirin sa na uku,” Inji shi
Comments 1