Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado-Bayero ya bukaci ‘yan siyasa da su guji siyasar zafin rai da tashin hankali.
Sarkin ya yi wannan jawabi ne a ranar Talatar nan a Kano a wajen kaddamar da takardar bukatu na ‘yan takara na jam’iyyun siyasa daban-daban, gabanin babban zabe na 2023.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa takardar, mai taken “Hasken Jihar Kano Project”, Partnership to Engage, Reform and Learn (PERL) ce ta kaddamar da ita.
Ofishin harkokin Ƙasashe rainon ingila na Ƙasashen Waje (FCDO) ne ya tallafawa shirin.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Sarkin wanda ya samu wakilcin Alhaji Habib Bello-Dankade, ya ce tashin hankali ba shi da wani amfani, sai dai illa.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/alummar-anambra-sun-shiga-fargaba-saboda-barazanar-ambaliyar-ruwa/
Ado-Bayero ya kuma shawarci PERL da su yi amfani da kafafen yada labarai wajen fadakar da mutane kan aikin.
Malam Isa Surajo, shugaban kungiyar PERL na jihar Kano da Jigawa, ya bayyana cewa wannan tsari ne mara bangaranci da ke fadada tasirin ‘yan kasa a harkokin mulki.
Ya ce ana yin hakan ne ta hanyar tsara ajandar hada hadar bukata ga ‘yan takara.
“Takardar ta bayyana tsare-tsaren tunkarar zabe da kuma bayan zabe kan ilimi, lafiya, noma da muhalli.
“Sauran fannonin su ne kasuwanci, mata da mutanen da ke da bukatu ta musamman, tattalin arziki na zamani da adalci da sauransu.
“Yana nufin fadada tasirin ‘yan ƙasa a kusa da hanyoyin gudanar da mulki don inganta isar da sako.
“Tsarin ajandar yana daya daga cikin abubuwan da suka sa a gaba wajen tabbatar da cewa an tallafawa ’yan kasa da kuma tsara su don ba da fifikon bukatunsu da bunkasa sharudda.
“Za su hada da ‘yan takarar don nuna musu bukatunsu lokacin da aka zabe su a ofisoshi da kuma yadda za su iya biyan wadannan bukatu a harkokin mulki,” in ji shi.
Shima da yake jawabi, Dr Auwalu Halilu, ya ce kusan kungiyoyi 60 ne suka shiga aikin samar da takardar.
Halilu ya ce takardar ta kunshi bukatu na gaba daya da duk bukatu a fadin kananan hukumomin jihar 44 da kuma shawarwarin yadda za a cimma su.
NAN ta ruwaito cewa a bangaren ilimi, wasu daga cikin matsalolin da aka bayyana sun hada da rashin isassun kayan koyo da koyarwa, yawan dalibai a aji, rashin isassun malamai da tsarin da sauransu.
A kan kiwon lafiya, batutuwan sun hada da nakasu na ma’aikata, rashin fitar da kudade don shirye-shiryen kiwon lafiya da kuma karancin kayan aiki, da sauransu.
An kuma gano ire-iren wadannan matsaloli a wasu sassa yayin da aka ba da mafita kan yadda mafi kyawu da masu rike da mukaman siyasa za su iya tunkarar su bayan zaben.
Wasu daga cikin mahalarta taron sun hada da wakilai daga masarautu biyar, kungiyoyi, wakilan jam’iyyun siyasa, kungiyoyin farar hula, masu bukata ta musamman da kungiyoyin kwararru da dai sauransu.
(NAN)